19 Afirilu 2021 - 14:39
Iran Ta Tabbatar Da Bude Da Tattaunawa Da Saudiyya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya tabbatar da bude tattaunawa da kasar Saudiyya ta hanyar shiga tsakanin kasar Iraki, sannan ya kara da cewa;

ABNA24 : Tattaunawar za ta amfani dukkanin kasashen biyu da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin wannan yankin."

Dan gane da tattaunawar da ake yi a birnin Vienna akan yarjejeniyar Nukiliyar Iran, Khatibzadeh ya ce; Kwararru ne su ke tattaunawar, kuma manufarta lalubo hanyar cirewa Iran takunkuman da aka kakaba ma ta da kuma komawar Amurka cikin yarjejeniyar.

342/